Shekaru da dama ya kwashe yana jagorantar ƙasarsa a cikin yanayi mai cike da matsin lamba da ƙalubale. Duk da takunkumi da barazanar da ake ta yi masa, bai taɓa nuna alamun rauni ko ja da baya ba. Bai amince da wata yarjejeniya da zai ga za ta rage martabar ƙasarsa ba, kuma bai taɓa rusuna wa matsin lambar ƙasashen Yamma ba. Ya tsaya da ƙafafunsa biyu wajen fuskantar ƙalubalen manyan ƙasashen duniya ba tare da tsoro ba. Ya gwammace ya tinkari adawa kai tsaye maimakon ya miƙa wuya. Har zuwa ƙarshen rayuwarsa, ya ci gaba da riƙe akidarsa da tsayin daka ba tare da sauya matsayi ba. Da yawa sun yarda cewa ya nuna jaruntaka fiye da mutane da dama. Ba a san shi da guduwa daga ƙalubale ko tsoron fuskantar gaba ba. A ƙarshe, rayuwarsa ta kasance sadaukarwa ga abin da ya yi imani da shi da kuma martabar ƙasarsa. Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un. اللهم تقبله في الشهداء